Friday, 28 September 2018

Kalli jirgin saman da yayi hadari amma babu wanda ya rasu a ciki

Wani jirgin sama yayi hadari inda ya fada cikin ruwa a kasar New Guinea, saida cikin ikon Allah babu wanda ya samu rauni ko kuma rasa ransa a cikin jirgin dake dauke da fasinjoji 35 da kuma ma'aikatan jirgin 12.


Ga rahoton BBChausa akan wannan hadari.

Wani jirgin fasinja ya fado daga sama a teku kusa da filin jirgin sama na Chuuk International Airport na Micronesia bayan da ya kasa sauka.

Hotunan jirgin sun rika zagayawa a shafukan sada zumunta daga Papua New Guinea, inda suka nuna jirgin yana zaune cikin ruwa kusa da gabar teku.

Amma babu wanda aya sami rauni cikin fasinjoji 35 da ma'aikatan jirgin 12 a jirgin mai lamba ANG73.

Ba a san dalilin da ya janyo wannan hatsarin ba, amma ana sa ran za a gudanar da bincike nan ba da dadewa ba.
Manajan filin jirgin sama na Chuuk, Jimmy Emilio ya sanar da BBC cewa jirgin ya fada cikin teku kimanin yadi 160 daga titin filin jirgin saman.

Manajan ya ce, "An tafi da wadanda ke cikin jirgin mai samfurin Boeing 737-800 zuwa asibiti kuma an duba su, inda aka tabbatar dukkansu na cikin koshin lafiya."
Jirgin ya taso ne daga tsibirin Pohnpei na Micronesia zuwa Port Moresby, babban birnin Papua New Guinea, amma ya tsaya a tsibirin Weno akan hanyarsa.


No comments:

Post a Comment