Monday, 10 September 2018

Kalli wani zane me magana kan bashin da China zata ba Afrika

Kasashenn Afrika da damane suka halarci taron hadin kai da kasar China kwanannan inda kasar Chinar tace ta ware zunzurutun kudi har dala miliyan dubu 60 dan tallfawa kasashen na Afrika dasu.


Duk da kasar ta China ta bayyana cewa babu wani sharadin siyasa akan bashin amma masu sharhi na ganin cewa akwai rina a kaba a wannan huldar ta tsakanin Afrika da China wanda ba lallai aga illar abin yanzu ba.

Shuwagabannin nahiyar da suka halarci taron dai sunyi na'am da wannan tallafi na kasar ta China.

No comments:

Post a Comment