Sunday, 2 September 2018

Karanta labarin wani Soja da Boko Haram suka kashe me ban tausai

Wannan jami'in soja ya rasa ranshi a fagen daga, jiya matarshi mai suna Firdausi Adam ta fitar da sanarwa a shafinta na facebook mai cike da tausayi.Ta ce ba ta san mai za ta fara fadi ba, mijinta soja ya mutu a fagen daga, ya bar ta da jariri dan wata biyu wanda bai taba ganin jaririn ba ma, wato an haifa masa jaririn lokacin yana fagen daga, ya sanar da ita cewa zai dawo gida sati mai zuwa don ya ga sabon jaririnsa ashe bai sani ba kwanansa ya kare ba zai sake dawowa gida ba har abada.

Allah Ka jikan wanna jarumin soja, Allah Ka karbi shahadarsa, Allah Ka saka masa da Aljannah mafi daukakiya, Allah Ka kula masa da jaririnsa da ya bari da duk wadanda suke karkashin ciyarwansa.
rariya.

No comments:

Post a Comment