Wednesday, 12 September 2018

Karanta sha tara ta arziki da mutumin Kano yawa magenshi da ya baiwa mutane mamaki

Wani matashi dan jihar Kano me suna Habibu Muazu Yahaya yayi abinda ba'a saba gani ba a Arewacin Najeriya, Habibu nada wata mage da ya matukar saba da ita wadda yake kira da sunan Sweety.Yanan kula da ita sosai, dan kuwa yayi ikirarin cewa a kullun rana ta Allah yana kashe mata kudi kimanin naira dubu daya wajan saya mata madara da kifi, yace, yayi kiwon dabbobi kala-kala tun yana dan karamin yaro amma be taba jin wadda ya saba da ita ba kamar Sweety.

Habibu yace a matsayinshi na musulmi yasan ko da yaushe mutuwa zata iya riskarshi kuma yana tunanin da wuya 'yan uwanshi su ci gaba da baiwa Sweety irin kulawar da yake bata, dan hakane ya yanke shawarar rubuta wasiyyar cewa idan ya mutu a baiwa Sweety kaso 20 cikin 100 na dukiyarshi dan a samu kudin kulawa da ita.

Irin wannan abu dai ba abin mamaki bane a kasashen turawa amma a nan gida Najeriya musamman Arewa abune wanda za'ace ya zama banbarakwai, Habibu ya kara da cewa damuwarshi yanzu shine da wuya 'yan uwanshi su yarda su baiwa Sweety wannan gado da ya bar mata.

Kafar BBC Pidgin ce ta yi hira da Habibu a Kano, dan haka ta nemi wasu lauyoyi inda ta tuntubesu akan wannan batu, lauya na farko ya shaida mata cewa, Magen ba zata samu wannan gado ba saboda a dokar Najeriya mutanene kawai ke iya yin gado banda dabbobi kamar yanda yake a dokokin kasahen turawa.

Saidai lauya na biyu yace, koda a dokar Najeriya ai akwai inda ake yarda da tsari irin na addinai da al'adun gargajiya kuma akwai dokar da ta yadda da wasiyya dan haka magen zata iya cin wannan gado

No comments:

Post a Comment