Friday, 14 September 2018

Karanta yanda aka samu Messi yanata rusa kuka

Tauraron dan kwallon kafar kungiyar Barcelona, Lionel Messi ya samu nasara sosai a kungiyar shi ta Barca inda ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon Duniya ta Ballon d' Or har sau biyar, saidai abin da ke ci mishi tuwo a kwarya shine rashin lashe wani gagarumin kofi ko daya da kungiyarshi ta kasar Argentina.


Tsohon me horaswa na kungiyar Barcelona da Argentina, Elvio Paolorosso ya bayyanawa manema labarai cewa, bayan da kasar Argentina ta yi rashin nasara a wasan karshe na cin kofin Copa America na shekarar 2016 a hannun kasar Chile, ya iske Messi can a dakin ajiye kaya shi kadai yana ta rusa kuka kamar karamin yaron da mahaifiyarshi ta rasu.

Yace, babu me rarrashinshi dan haka ya rugumeshi kuma suka dan sha giya tare.

No comments:

Post a Comment