Monday, 10 September 2018

Kasashen Rasha, Iran, da Turkiyya sun daina amfani da dalar Amurka

Kasashen Turkiyya, Rasha da Iran sun aminta akan yin cinikayya a tsakaninsu ta amfani da kudaden kasashen uku maimakon dalan Amurka.


Shugaban babban bankin Iran Abdolnaser Hemati ya bayyana wa manema labarai da cewa zasu gudanar da taro da shugabanin manyan bankunan Turkiyya da Rasha nan bada jimawa ba domin tabbatar da yunkurin.

Shugaban bankin ya bayyana hakan ne a lokacin da kasashen uku ke gudanar da taro a Tehran akan Siriya da ya samu halartar shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdo─čan da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.

Ya bayyana cewar sun aminta akan gudanar da kasuwancin man fetur, iskar gas da kuma banki ta amfani da kudaden kasashen maimakon dalar Amurka.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment