Monday, 10 September 2018

Ko shekaru 20 Buhari zai yi yana mulki ba zai iya gyara Najeriya ba>>Bafarawa

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato kuma me muradin tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana shugaba Buhari da cewa shugabane wanda be san yanda harkar tattalin arzikin kasa ke tafiyaba.


Bafarawa yace, ko da shekaru 20 za'a baiwa Buhari ba zai taba iya warware matsalolin kasarnan ba, Bafarawa yayi wannan magane a jihar Imo a ci ganba da neman goyon bayan jama'a a kan muradinshi na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Ya kara da cewa, alamar cewa Buhari bai san ta kan mulki ba shine bashin da yake ciyowa daga kasar China, wanda idan ba'a yi hankali ba zai iya jefa kasarnan cikin matsala.

Ya kuma ce, abin takaicine yanda aka mayar da 'yan adawa masu cin hanci ake musu cinne da EFCC amma da mutum ya shiga APC shikenan ya tsira.

No comments:

Post a Comment