Tuesday, 11 September 2018

Ku sayawa matasa fom da kudin ta kuka tara da niyyar saya min fom>>Shugaba Buhari ya gayawa sauran kungiyoyi

A jawabin da yayi lokacin amsar fom din takara da kungiyar NCAN ta saya mishi, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya mika godiyarshi a garesu sannan ya bayyana cewa, tun bayan da jam'iyyar su ta APC ta fadi kudin sayen Fom ya kuma nuna rashin amincewarshi akan tsadar fom din kungiyoyi da dama sun nuna son saya mishi fom din.


Shugaba Buhari yace, kungiyoyi kamar na, manoma shinakafa dana 'yan kasuwar man fetur dana masu yin takin zamani dadai sauransu duk sun bayyana cewa suna son saya mishi fom din.

Amma yace ya yadda dana wannan kungiya ta NCAN dan haka yana kira ga sauran kungiyoyin da su yi amfani da kudin da suka tara da niyyar saya mishi fom din wajan sayawa matasa dake son tsaya takara fom.

Shugaba Buhari yace akawai matasa hazikai masu kishin kasa dake son tsayawa takara amma saboda rashin kudi basu iya fitowa dan haka yayi kira ga wadannan kungiyoyi da su tallafawa irin wadannan matasa.

No comments:

Post a Comment