Wednesday, 12 September 2018

Kuma dai: Kungiyar manona shinkafa sun bayar da gudunmuwar miliyar 56 dn sayawa shugaba Buhari Fom

Bayan da kungiyar NCAN ta sayawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari fom din sake tsayawa takara akan kudi Naira miliyan 45, kungiyar manoman shinkafa itama ta bayar da gudummuwar Naira miliyan 56 dan sayawa shugaba Buharin fom.
Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Atiku Bagudu ne ya bayyana haka inda yace ya wa manona shinkafar jagora zuwa gurin shugaban APC na kasa dan kai wannan gudummawa.

Saidai a jawabinshi a gurin karbar fom din da NCAN suka saya mishi, shugaba Buhari yayi rokon cewa duk sauran kungiyoyi dake son saya mishi fom su yi amfani da kudin da suka tara wajan sayawa matasa masu son tsayawa takara fom din.

No comments:

Post a Comment