Sunday, 16 September 2018

Kungiyar Matasan Arewa Ta Bukaci Gwamnati Ta Gaggauta Kamo Matasan Biafra Wadanda Suka Kai Farmarki Akan Dukiyoyin 'Yan Arewa A Garin Fatakwal

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Jihohin Arewa 19, sun yi kira da babbar murya ga Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Buhari da cewar, cikin gaggawa a gaggauta kamo Matasan Inyamurai 'yan tawayen Biafra, wadanda suka kaddamar da hari akan 'yan Arewa da dukiyoyinsu a garin Fatakwal domin fuskantar hukunci. 


Shugaban gamayyar Kungiyoyin Matasan Alhaji Yerima Shetima yayi wannan kiran, a yayin wata ganawa do manana labarai da yayi a Kaduna, domin nuna damuwa da alhinin Matasan Arewa akan aikin dabbanci da 'yan tawayen Biafra suka yi, wadanda ya bayyana a matsayin fitinannu marasa son zaman lafiya. 

Yerima Shetima ya cigaba da cewar, kiran ya zamo wajibi bisa la'akari da yadda babban zabe na shekarar 2019 ke kara karatowa, sannan Matasan Inyamuran ke kokari hasa wutar fitina, kuma rashin daukar matakin da ya dace daga gwamnati, zai sanya 'yan tawayen su ji dadi sannan su cigaba da farmakar 'Yan Arewa mazauna kudancin Nijeriya, kuma hakan zai haifar da daukar fansa ta ramuwar gayya daga bangaren Matasan Arewa akan Inyamurai mazauna Arewacin Nijeriya, lamarin  da zai kara dagula zaman lafiyar Nijeriya a samu matsaloli manya a yayin gudanar da babban zabe na kasa dake tafe 2019, lallai dole Gwamnati ta dauki matakin hana faruwar hakan. 

Shugaban Matasan Arewacin Nijeriyan, ya kuma soki lamirin shugabannin kudancin Nijeriya wadanda suka fito kararar suka zargi Buhari da cewar ya nada Dan Arewa a matsayin sabon shugaban DSS, inda yace kalaman na 'yan kudu shirme ne da kuma rashin adalci, domin shugaban kasa shine yake da hurumi na sanya amintaccen da ya amince da shi a matsayin shugaban DSS, kasancewar wuri ne mai matukar muhimmanci da ke bukatar mutum mai amana, kuma dukkanin shugabannin  da akayi a baya kowa ya sanya wanda ya amince da shi ne a matsayin shugaban DSS, tun daga kan Obasanjo har ya zuwa 'Yar Aduwa da Jonathan kowa yayi amfani da na shi ne, saboda haka babu dalilin sukar Buhari akan zabin da yayi na sabon shugaban DSS. 

Yerima Shetima wanda tuni ya bayyana aniyarshi ta neman kujerar Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar karamar hukumar Kaduna ta Arewa a karkashin jam'iyyar PDP, yace babban abinda ya ja hankalin shi ga siyasa shine, domin bayar da tashi gudummuwa wajen kare martaba da mutuncin Arewa, da dawowa Arewa da martabar ta a majalisa, sakamakon yadda akasarin wakilai daga Arewa suka zama 'yan dumama kujera da rashin yin wani katabus na cigaban Arewa a majalisa, inda ya shawarci jama 'ar Arewa dasu dubi cancanta a yayin zabukan dake tafe, su zabi mutane nagari wadanda zasu kare muradun su a majalisa, inda ya bada tabbacin kawo sauyi mai ma 'ana  ga jama 'ar mazabar Kaduna ta Arewa da jihar Kaduna da yankin Arewa da Nijeriya baki daya idan Allah ya kaishi Majalisa.
Rariya.

No comments:

Post a Comment