Friday, 14 September 2018

Kungiyar 'yan kudu da tsakiyar Najeriya sun caccaki shugaba Buhari akan nadin sabon shugaban DSS

Kungiyar mutanen kudu da tsakiyar Najeriya sun soki shugaban kasa, muhammadu Buhari saboda nadin sabon shugaban hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS da yayi jiya inda ya nada Yusuf Magaji Bichi wanda ya fito daga jihar Kano.


Kungiyar tace ba'a taba shugaban kasar da ya raba kawunan mutane a Najeriya irin shugaba Buhari ba kuma irin wannan nadi na son kai da yayi ya nuna karara cewa mutanen yankinshi yake ba fifiko a wajen bayar da mukaman gwamnati.

Kungiyar ta kara da cewa, ko kusa mutumin da Buhari ya nada be kai me rikon shugabancin hukumar ba, Matthew Seiyefa kwarewa da gogewa a iya aiki ba sannan kuma yawancin mutanen da ke karkashin korarren shugaban DSS Lawal Daura 'yan kudune shi yasa Buhari ya fita waje ya nemo wanda yayi ritaya ya bashi mukamin.

The Cable ta ruwaito kungiyar na cewa ta yi fatali da wannan nadi kuma basu jin nauyin fadawa Buharin cewa Najeriya bata samu hadin kai ba a karkashinshi.

No comments:

Post a Comment