Sunday, 16 September 2018

Kura ta kwance: Ronaldo ya ciwa Juventus kwallaye a karin farko

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo ya ciwa sabuwar kungiyar tashi kwallo a karin barko bayan buga wasanni uku tun bayan komawarshi kungiyar, Ronaldon ya ci kwallaye 2 a wasan da Juventus ta buga yau Lahadi da kungiyar Sassuolo. Wasan ya kare Juventus na cin Sassuolo 2-1.Wasu dai sun fara cewa, kwallon da Ronaldon yaci ta farko kwalloce me sauki sosai wadda har suna cewa wai itace kwallo mafi sauki da ya taba ci a tarihin kwallonshi saboda ta sameshine kuma daga shi sai raga amma hakan be hanashi nuna murnarshi sosai ba sannan kuma ya kara ta biyu.

Masu sharhi na ganin cewa, daga yanzu Ronaldon zai fara ciwa Juventus din kwallaye babu kakkautawa.

Kamin cin wadannan kwallaye, Ronaldo ya shafe mintuna sama da dari 3 yana gwagwarmaya a Juventus din sannan kuma ya zazzaga shatashatai 27.


No comments:

Post a Comment