Tuesday, 11 September 2018

Kwankwaso, Atiku, da Saraki sunki amincewa da fitar da dan takara ba tare da zaben fidda gwani ba

Kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP ya shirya wani kwamiti na musamman dan tattaunawa da masu neman tikitin jam'iyyar dan tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben shekarar 2019.


Shugaban kwamitin amintattun na PDP Walid jibrin ne ya bayyanawa manema labarai haka, kamar yanda jaridar Punch ta ruwaito, ya kara da cewa, sun ja kunnen membobin kwamitin akan su yi hankali kada su buge da yiwa ko wane dan takara kampe su yi aikinsu ba tare da nuna fifiko ba.

Saidai manyan 'yan takara uku a jam'iyyar sunki amincewa da wannan yunkuri.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da kakakin majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki duk sunce basu yadda da wannan mataki ba, sun fi so a yi zaben fidda gwani domin kowannensu yana tunanin shine yafi cancanta da zama dan takarar.

Saidai jaridar Punch tace, data tuntubi bangaren Sanata Ahmed Makarfi wanda shima yana cikin 'yan takarar, sunce su ba zasu ce komi akan wannan batun ba tukuna.


No comments:

Post a Comment