Friday, 28 September 2018

Kwankwaso ya samu kyakkyawar tarba a jihar Jigawa>>Zanyi nasara akan Buhari idan na samu tikitin PDP>Injishi

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara jihar Jigawa a jiya, Alhamis kuma ya samu kyakyawar tarba daga al'ummar jihar inda sukayi dandazo a gurin da ya gabatar da taron kamfe.

A ziyarar da ya kai jihar Filato kuwa, Sanata Kwankwaso yace idan PDP ta bashi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa to tabbas zai kayar da shugaba Buhari a zaben 2019.

Ya kara da cewa ya fito ne daga jihar dake da yawan al'ummar da zasu yi tasiri sosai wajan canja sakamakon zabe sannan kuma yana da goyon baya daga yankunan Arewa maso yamma kuma idan aka bashi tikitin yasan masoyan nashi zasu karu.

Kwankwaso yace idan aka zabeshi zai warware matsalolin Najeriya, musamman harkar ilimi yace zai bayar da ilimi kyauta kamar yanda yayi a jihar Kano kuma zai samar da ayyukan yi da tsaron lafiya da dukiyoyin Al'umma, kamar yanda Vanguard ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment