Thursday, 13 September 2018

Kwankwaso yayi kira ga sauran 'yan takarar PDP su hada kai dan kawar da Buhari

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga sauran abokan takararshi na PDP da su hada karfi waje guda dan ganin sun kayar da shugaba Buhari a zabe ne zuwa.


Kwankwaso yace yayi nadamar bin Buhari a shekarar 2015 wajan kafa gwamnati saboda ba irin canjin da yayi tsammanin za'a kawo ba aka kawo, maimakon haka sai rashin aikin yi ya karu,kashe-kashe da yunwa da talauci suka karu a kasarnan.

Ya kara da cewa wannan daliline yasa ya fito takara dan kawo canjin wannan hali da kasarnan ta fada a ciki.

Saidai Kwankwason yayi alkawarin goyawa duk wanda ya samu tikitin takarar na PDP baya dan ganin an kawar da gwamnatin APC.

No comments:

Post a Comment