Tuesday, 4 September 2018

Kylian Mbappe na gab da yin abinda wani dan kwallo be taba yi ba a tarihi

Tauraron dan kwallon kafar PSG, Kylian Mbappe na kan hanyar zama dan wasan kwallon kafa na farko a Duniya da zai lashe kyautar tauraron matashin dan wasa sau biyu a jere, Mbappe ne dai ya lashe kyautar a bara kuma a wannan shekarar ma shine ake tunanin zai lasheta.


Kyautar da 'yan jaridun kwallo ke baiwa tauraron matashi dan wasan da yafi nuna gwaninta a kakar wasa ana bayar da ita ne ga 'yan kwallo da bai wuce shekaru 21 da haihuwa ba kuma dole ya kasance dan kwallon na wasa a daya daga cikin kungiyoyin kasashen turai.

A tarihin kyautar, babu dan kwallon da ya taba daukarta sau biyu, wadanda suka dauki wannan kyauta a shekarun baya sun hada da Paul Pogba da Wayne Rooney da Sergion Aguero, Lionel Messi da kuma Rafael Van der Vaart wanda shine ya fara lashe kyautar.

Masu sharhi da dama na ganin cewa Mbappe ne zai lashe wannan kyauta ta 2017/18 saboda irin rawar da ya taka wajan taimakawa kasarshi lashe kofin Duniya da kuma rawar ganin da ya taka a kungiyarshi ta PSG.

A cikin wanda aka fitar da sunayensu da zasu iya lashe wannan kyauta akwai dan shugaban kasar Liberia wanda shima tsohon tauraron dan kwallon kafane, Timothy Weah.

Ga jerin sunayen 'yan kwallon da aka fitar dan lashe wannan gasa kamar haka da kuma kungiyoyin da suka fito:

Carles Alena (Barcelona)
Trent Alexander-Arnold (Liverpool)
Kelvin Adou Amian (Toulouse)
Houssem Aouar (Lyon)
Musa Barrow (Atalanta)
Sander Gard Bolin Berge (Genk)
Justin Bijlow (Feyenoord)
Abdelkader Brahim Diaz (Manchester City)
Josip Brekalo (Wolfsburg)
Patrick Cutrone (AC Milan)
Dani Olmo (Dinamo Zagreb)
Thomas Davies (Everton)
Mattijs de Ligt (Ajax)
Moussa Diaby (PSG)
Diogo Dalot (Manchester United)
Moussa Djenepo (Standard Liege)
Ritsu Doan (Groningen)
Eder Militao (Porto)
Odsonne Edouard (Celtic)
Evander (Midtjylland)
Phil Foden (Manchester City)
Juan Foyth (Tottenham)
Gedson Fernandes (Benfica)
Nicolas Gonzalez (Stuttgart)
Achraf (Borussia Dortmund)
Amadou Haidara (Red Bull Salzburg)
Kai Havertz (Bayer Leverkusen)
Jonathan Ikone (Lille)
Joao Filipe (Benfica)
Jovan Cabral (Sporting Club)
Dejan Joveljic (Red Star)
Boubacar Kamara (Marseille)
Yann Karamoh (Bordeaux)
Moise Kean (Juventus)
Jules Keita (Dijon)
Justin Kluivert (Roma)
Teun Koopmeiners (AZ Alkmaar)
Alban Lafont (Fiorentina)
Leo Jaba (PAOK)
Mikhail Lysov (Lokomotiv Moscow)
Jean-Victor Makengo (Nice)
Manu Garcia (Toulouse)
Mauro Junior (PSV Eindhoven)
Kylian Mbappe (PSG)
Weston McKennie (Schalke)
Evan N'Dicka (Eintracht Frankfurt)
Pietro Pellegri (Monaco)
Ronael Pierre-Gabriel (Monaco)
Christian Pulisic (Borussia Dortmund)
Ruben Vinagre (Wolves)
Marcelo Saracchi (RB Leipzig)
Ismaila Sarr (Rennes)
Ryan Sessegnon (Fulham)
Anthony Moya Vega (Atletico Madrid)
Dayot Upamecano (RB Leipzig)
Federico Valverde (Real Madrid)
Vinicius Junior (Real Madrid)
Moussa Wague (Barcelona)
Timothy Weah (PSG)
Luca Zidane (Real Madrid)

No comments:

Post a Comment