Friday, 28 September 2018

LADO YA JANYE TAKARARSA YA MARA SHEKARAU BAYA

Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Bashir Garba Lado ya janyewa tsohon Gwamnan Kano  Malam Ibrahim Shekarau, takarar daya ke nema ta kujerar Kano ta Tsakiya.


Tun bayan da Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana Malam Shekarau a matsayin dantakarar Sanatan Kano ta Tsakiya Lado ya bayyana kin amincewarsa Inda yaci gaba da Neman takararsa.

 Sai dai kuma yau babban daraktan yakin Neman zabensa kuma me bawa Gwamna shawara akan al'amuran siyasa Alh Mustapha Hamza Buhari Bakwana ya bayyana cewa lado ya hakura da takarar Sanata zai marawa Malam Ibrahim shekarau baya har ya bada gudunmawar motoci kirar Sharon guda 25 ga Buhari da Ganduje da Shekarau.

Alh Hamza Bakwana ya bayyana hakan ne yau a yayin mubayi'a da kananan hukomomin Dawakin Kudu Warawa da Gwale da kuma Kumbotso da Tarauni suka kawo Malam Shekarau a Mundubawa Gidan Sardaunan Kano.
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment