Tuesday, 4 September 2018

Madrid zasu yi musayar Marcelo da Alex Sandro na Juventus

Ga dukkan alamu dai maganar komawar Marcelo Juventus daga Real Madrid na so ta tabbata, domin kuwa rahotanni sun bayyana dake nuna cewa, Real Madrid din zasu yi musayar Marcelo da dan wasan baya na Juve, Alex Sandro.


Jaridar Tuttosport ta kasar Italiyace ta bayyana wannan labari inda tace Marcelon dama yana son bin tsohon abokin aikinshi, Ronaldo zuwa Juven wanda sun shaku da juna a Real Madrid.

Haka kuma rahoton ya bayyana cewa, dangantaka ta fara yin tsami tsakanin sabon me horas da 'yan wasa na Madrid din, Julen Lopetegui da Marcelo, hakan kuwa ya fito filine bayan da ya canja Marcelo a wasan da Madrid din ta buga da Girona.

Wanda bayan wasan, Marcelo ya bayyanawa manema labarai cewa, baiji dadin canjin da aka mishi ba kumama bai san dalilin da yasa aka canjashiba dan yana son ya ci gaba da wasa amma dole ya yiwa kocin biyayya.


No comments:

Post a Comment