Monday, 10 September 2018

Majalisun Tarayyar Najeriya sun dage dawowarsu hutu

Hadakar Majalisun Tarayyar Najeriya sun dage dawowarsu daga hutu zuwa sati na biyu na watan Oktoba mai zuwa sabanin 25 ga watan Satumbar nan da tun farko aka tsara dawowarsu.


Rashin dawowar Majalisun daga hutu akan lokaci na barazana ga kasafin kudin hukumar zaben Najeriyar da ke neman sahalewar majalisar a dai dai lokacin da babban zaben kasar ke karatowa.

Rahotanni na nuni da cewa abu ne mai wuya kwamitin kasafin kudin majalisun sun kammala bibiyar kunshin kasafin kafin karshen watan Satumba, matakin da ke barazana ga yiwuwar gudanar da zaben a lokacin da hukumar ta INEC ta tsara.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment