Saturday, 29 September 2018

Marafa ya janye daga zaben fitar da gwani a Zamfara

An samu rabuwar kai a tsakanin gangamin mutum takwas da aka fi sani da G8 masu neman takarar gwamna a karkashin jam`iyyar APC a Zamfara.


Kawancen 'yan takarar ya rabu biyu wadanda ke zazzafar hamayya da mutumin da gwamnan jihar Abdul`aziz Yari ke mara wa baya.

Wani bangare mai mutum uku, ciki har da Senata Kabiru Marafa ya sanar da janyewa daga zabin fida-da-gwanin da ake sa ran yi ranar lahadi.

Senata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa sun janye ne saboda karar da ya shigar a kotu inda yake kalubalantar shugabancin jam'iyyar APC a jihar.

Daga cikin mutum uku da suka janye daga kawancen 'yan takarar guda takwas sun hada da Eng Abu Magaji da Sagir Hamidu.

Sanata Marafa da ke magana da yawun sauran 'yan takarar guda uku ya ce sun janye ne domin bin umurnin kotu.

Bangaren Sanata Marafa da ke wakiltar Zamfara ta tsakiya kuma da ke hamayya da bangaren gwamnati sun zabi nasu shugabannin jam'iyya ne na daban a matakin mazabu da kananan hukumomi da kuma na jiha, dalilin da ya sa ya shigar da kara.

Shugabannin da uwar jam'iyya ta amince da su, su ne za su fitar da 'yan takara, inda Marafa ke ganin bangaren gwamnati ba za su fitar da sunan shi ba a matsayin dan takarar kujerar da yake nema ta gwamna.

"Kotu ta ce mu tsaya a matsayinmu kada mu yi komi, haka su ma su tsaya ba tare da yin komi ba" in ji shi.

Ya kuma ce idan har aka gudanar da zaben, to za su ruga kotu su sanar da ita cewa an saba dokarta.

Rikicin siyasa a Zamfara ya kara zafi ne bayan da Gwamnan jihar Abdul'aziz Yari Abubakar ya sanar da goyon bayansa ga kwamishinansa na Kudi Kogunan Gusau Alhaji Muktar Shehu Idris a matsayin wanda zai gaje shi.

Wannan ne ya sa wasu daga cikin masu sha'awar takarar gwamnan a jam'iyyar APC su takwas da suka hada da mataimakin gwamnan Ibrahim Wakalla da kuma Ministan tsaro Mansur Dan Ali suka hade kai domin yakar gwamnan na Zamfara.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment