Friday, 28 September 2018

Maryam Booth ta fara aikin yiwa Atiku Kamfe

A makon da ya gabatane muka ji labarin tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth ta samu babban mukami daga dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP  watau Atiku Abubakar inda ya bata mataimakiyar shugaban gidauniyar shi ta tallafawa gajiyayyu, yankin Arewa.


Maryam din tuni ta kama aiki inda ta fara yiwa Atikun yakin neman zabe.

A wannan hoton na sama itace tare da mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben Atikun, Godsday Orubebe da kuma shugaban gidauniyar tallafawa gajiyayyun ta Atiku, Aliyu Bin na Abbas.

No comments:

Post a Comment