Saturday, 15 September 2018

Mata sun samu damar fara tuka jiragen sama a Saudiyya

Wani kanfanin jiragen sama dake Saudiyya mai suna Flynas ya yada a shafinsa na twitter da cewa zai dauki mata a matsayin mataimakan matuka jiragen sama da kuma ma’aikatan cikin jirgi.


Sanarwar ta nemi mata da ba su wuce shekaru 35 ‘yan kasar Saudiyya dake da takardar shedan kammala sakandare da kuma takardan kammala karatun lamuran jirage da gabatar da kansu domin aikin.

Kanfanin dillancin labaran  Sabq ya rawaito cewa kanfanin Flydeal din zai debi ma'aikata mata 20 da maza 15 a matsayan wadanda zasu rinka gudanar da aiyuka cikinjirgi.

Wannan ne dai karon farko da mata zasu fara aiki a matsayin matuka da masu aiki a cikin jirgi a kasar Saudiyya.

Sarki Salman bin Abdulaziz ya bayar da umurnin baiwa mata damar amfani da karafa a ranar 26 ga watan Satumba wacce ta fara aiki daga ranar 24 ga watan Yuni.

Saudiyya dai nada zummar kara yawan ma’aikata mata daga kaso 22 zuwa 30 a shekarar 2030.
TRThausa

No comments:

Post a Comment