Sunday, 9 September 2018

Matashiya ta farko a tarihin Najeriya daga jihar Sakkwato dake bautar kasa da digiri na uku

Kamar yadda aka sani, dalibai da suka kammala digiri na farko ne su kafi yawa cikin adadin masu yiwa kasa hidima a Najeriya. Wasu lokutan ana samun masu digiri na biyu (Msc) amma ba kasafai ake samun wadanda su ka gama digiri na uku wato (PhD) ba.Dr Zainab Adiya 'yar asalin jihar Sakkwato, wasu rahotannin na cewa itace mace na farko mai darajar karatu na PhD da ta fara yin hidimar kasa a Najeriya.

Sai dai sabanin wannan rahotannin an gano wata matashiya 'yar bautar kasa 'yar Arewa, Zainab Ibrahim Adiya, mai shekaru 27 wadda ta kammala digirin digiriri wato PhD a fanin 'Chemistry'.

Babu shakka wannan labarin wannan hazikar matashiyar na nuna cewa duk irin girman digirin da mutum ya mallaka, yana iya zuwa ya gudanar da hidimar kasar muddin shekarunsa basu haura 30 ba.

Labarin matashiyar na zuwa ne bayan mawaki Davido shima ya hallarci sansanin matasa masu yiwa kasa hidima a Legas inda ya yi rajitsan yiwa kasa hidimar. Hotunan Davido tare da sauran matasa masu bautar kasa ya karede shafukan sada zumunta da kafafen yadda labarai.

No comments:

Post a Comment