Wednesday, 12 September 2018

Messi ya cewa Barcelona ta gaggauta sayo Pogba

Tauraron dan wasan kungiyar Barcelona, Lionel Messi ya bukaci kungiyar da ta gaggauta sayo dan wasan Manchester United, Paul Pogba wanda shima rahotanni da dama suka tabbatar da cewa ya kagara ya bar kungiyar.


Saidai matsala daya da Barcelona zata fuskanta a yanzu da zata hanata sayo Pogba itace, dokar nan ta hana kashe kudi fiye da kima ta hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA wadda ta kayyade iya yawan kudin da kungiyar kwallo zata iya kashewa wajan sayen 'yan wasa da gudanarwa kada su haura ribar da kungiyar ke samu.

Saidai nan da zuwa watan Janairu Barcelona na da damar amso Pogba a matsayin aro daga Man United din da kuma watakila damar sayenshi a karshe. Wannan zai iya faruwa kenan idan basu samu madadinshi ba kamin zuwan lokacin ko kuma ita Man U din ta yadda ta bayar dashi, kamar yanda express ta UK ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment