Tuesday, 25 September 2018

Messi ya zabi Ronaldo a matsayin gwanin FIFA amma Ronaldon be zabeshi ba:Kalli yanda aka gudanar da zaben

Bayan da aka kammala bayar da kyautukan gwarazan 'yan kwallon FIFA na kakar wasa ta 2017/18 wanda dan wasan Madrid, Luka Modric ya lashe kyautar gwarzon dan kwallo a ajin maza inda ya doke Ronaldo da Salah, FIFA din ta bayyana yanda aka yi zaben gwanayen nata.


Yanda ake zaben gwanin dan kwallon FIFA shine.

'Yan jaridu zasu bayar da kuri'u kashi 25 cikin dari.

Sai kuma masu horas da 'yan wasa na kasashen da ke da wakilci a FIFA su bayar da kashi 25 cikin dari.

Sai kuma kaftin na kasashe suma su bayar da kashi 25 cikin dari na kuri'ar.

Sai kuma masoya kwallon kafa su bayar da sauran kashi 25 cikin darin.

Wani abu da ya dauki hankulan masoya kwallon kafa shine, a karin farko, Messi ya zabi Ronaldo a cikin mutum uku da yake tunanin sune gwarazan kwallon kafa na FIFA saidai shi Ronaldon be zabi Messin ba.

Bayanin da FIFA ta fitar ya bayyana yawan makin da 'yan wasa 10 da aka fitar suka samu kamar haka

1. Luka Modric (29.05)
2. Cristiano Ronaldo (19.08)
3. Mohamed Salah (11.23)
4. Kylian Mbappe (10.52)
5. Lionel Messi (9.81)
6. Antoine Griezmann (6.69)
7. Eden Hazard (5.65)
8. Kevin De Bruyne (3.54)
9. Raphael Varane (3.45)
10. Harry Kane (0.98)

Sannan kuma kaftin kaftin na kasashe sunyi zabe kamar haka:

Sunan dan wasane a farko sai kuma sunayen 'yan wasa uku da ya zaba a matsayin zabinshi na wanda yake ganin sune gwarazan 'yan kwallon na FIFA.

Lionel Messi - Luka Modric, Kylian Mbappe, Cristiano Ronaldo

Eden Hazard - Luka Modric, Raphael Varane, Kylian Mbappe

Miranda - Cristiano Ronaldo, Kylian Mbappe, Lionel Messi

Luka Modric - Raphael Varane, Cristiano Ronaldo, Antoine Griezmann

Harry Kane - Cristiano Ronaldo, Lionel Messi, Kevin De Bruyne

Manuel Neuer - Eden Hazard, Luka Modric, Raphael Varane

Hugo Loris - Raphael Varane, Antoine Griezmann, Kylian Mbappe

Giorgio Chiellini - Cristiano Ronaldo, Luka Modric, Mohamed Salah

Virgil van Dijk - Mohamed Salah, Kevin De Bruyne, Kylian Mbappe

Cristiano Ronaldo - Raphael Varane, Luka Modric, Antoine Griezmann

Robert Lewandowski - Luka Modric, Raphael Varane, Kylian Mbappe

Sergio Ramos - Luka Modric, Cristiano Ronaldo, Lionel Messi

Sai kuma masu horas wa na kasashe sunyi zabensu kamar haka:

Roberto Martinez - Luka Modric, Raphael Varane, Lionel Messi

Gareth Southgate - Luka Modric, Raphael Varane, Eden Hazard

Didier Deschamps - Antoine Griezmann, Raphael Varane, Kylian Mbappe

Joachim Low - Luka Modric, Kylian Mbappe, Eden Hazard

Roberto Mancini - Cristiano Ronaldo, Kylian Mbappe, Luka Modric

Alex Mcleish - Mohamed Salah, Eden Hazard, Luka Modric

Luis Enrique - Lionel Messi, Luka Modric, Mohamed Salah

Ryan Giggs - Luka Modric, Kylian Mbappe, Cristiano Ronaldo


No comments:

Post a Comment