Sunday, 16 September 2018

Ministar kudi, Kemi Adeosun, ta sulale bayan yin murabus

Tsohuwar minstar kudi, Kemi Adeosun, ta fice daga Najeriya kwana daya kacal bayan ta mika takardar barin mukaminta biyo bayan samunta da laifin karyar takardar bautar kasa.


Adeosun ta kasance ministar kudin Najeriya tun watan Nuwamba na shekarar 2015. Ta yi murabus daga mukaminta ne bayan jaridar Premium Times ta bankado cewar ministar ta gabatar da takardar bautar kasa ta bogi.

A ranar Jum'a, 14 ga watan Satumba, Mrs. Kemi Adeosun ta yi murabus daga kujerarta ta Ministar kudi, biyo bayan zarginta da ake yi na amfani da takardar shaidar yin bautar kasa ta bogi.

Wannan zargi ya dauki tsawon lokaci yana yawo a tsakanin jama'a, har sai ranar juma'a da Kemi ta kawo karshen shi ta hanyar sauka daga mukamin.

Karanta cikakkiyar wasikar da ta aikawa shugaban kasa Buhari, don sanar da shi matsayarta na yin murabus daga wannan mukami na ministar kudi.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment