Friday, 14 September 2018

MINISTAR KUDI TA YI MURABUS

Murabus din da Ministar Kudin Nijeriya, Misis Kemi Adewosun ta yi, ba ya rasa nasaba da takaddamar da ake yi game da ita akan takardar shaidar bautar kasa (NYSC), kasancewar ta yi karatu a kasar Turai wasu suka dago maganar cewa bata da takardar NYSC dan haka suka ce lallai Shugaba Buhari ya sallame ta.


Tun daga lokacin da aka fara maganar fadar Shugaban kasa bata ce komai akai ba, kwatsam yau sai aka ji cewa Ministar ta sauka daga mukamin ta, wasu bayanai sun nuna cewa hatta da safiyar yau an ganta tana aiki a ofis kafin sanarwar ta bayyana.

Sauran bayanan za mu ji nan gaba kadan idan fadar Shugaban kasa ta fitar da dalilin murabus din na Madam Kemi.
Rariya.

No comments:

Post a Comment