Sunday, 16 September 2018

Ministocin Buhari 3 da suka yi murabus bisa radin kan su

Ministoci 3 ne suka yi murabus don radin kan su tun bayan da shugaba Buhari ya nada su a shekarar 2015. Ministocin sune;


1. Kemi Adeosun: Uwargida Kemi Adeosun ta kasance ministar kudin Najeriya tun watan Nuwamba na shekarar 2015.

Ta yi murabus daga mukaminta ne bayan jaridar Premium Times ta bankado cewar ta gabatar da takardar bautar kasa ta bogi domin a nada ta minista.
2. Mista Kayode Fayemi: Zababben gwamnan jihar Ekiti, Mista Kayode Fayemi, ya yi murabus ne daga mukaminsa ministan ma'adanai da albarkatun kasa ranar 30 Mayu domin mayar da hankali a kan takarar kujerar gwamna da yake yi a wancan lokacin.

Kafin nada shi mukamin minista a gwamnatin APC, Mista Fayemi ya zama gwamnan jihar Ekiti daga shekarar 2010 zuwa 2014.
3. Amina Mohammed: Tsohuwar ministar muhalli daga watan Nuwamba na shekarar 2015 zuwa watan Disamba na shekarar 2016.

Amina tayi murabus ne daga gwamnatin shugaba Buhari biyo bayan bayan nada ta a matsayin mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya (MDD).
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment