Wednesday, 26 September 2018

Mourinho da Pogba sun yi sa-in-sa

Wani faifan bidiyo ya nuna Jose Mourinho da Paul Pogba suna sa-in-sa a wajen atisaye a ranar Laraba, kwana daya da kocin ya karbe mukamin mataimakin kyaftin daga dan wasan tawagar Faransa.


Mourinho bai saka Pogba a karawar da Derby County ta yi waje da Manchester United a Caraboa Cup a ranar Talata a Old Trafford ba.

Bayan da aka tashi daga fafatawar Mourinho ya tabbatar da karbe mataimakin kyaftin din United daga Pogba, amma ya musanta zargin cewar ya samu sabani da dan kwallon.

Derby ta yi nasara a kan United a bugun fenariti da ci 8-7, bayan da suka tashi wasa 2-2.
A ranar Asabar United za ta ziyarci West Ham United a gasar Premier wasan mako na bakwai.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment