Wednesday, 12 September 2018

Mourinho yayi tuntube, fuskarshi ta daki kasa

Me horas da 'yan wasa na kungiyar Manchester United, Jose Mourinho yayi tuntube ya ci kasa a ranar asabar din data gabata.


Mourinho ya je filin wasa na Wembley ne, Kasar Ingila inda aka buga wasa tsakanin kasashen igilar da Sifaniya, wasan da ya kare da sakamakon 2-1, Sifaniyar na cin Ingila.

Ya je tsallaka irin igiyarnan ce da ake sakawa a guraren taro dan kare wani bu ko yin hanya, sai kafarshi da baya ta makale akan igiyar, nan kuwa ya fadi kasa, wasu rahotannin ma sunce har fuskarshi sai da ta daki kasa.

Da taimakon wani ma'aikacin filin wasan, mourinho ya mike tsaye, bidiyon wannan abu yayi ta watsuwa a shafukan sada zumunta inda akaita kallo.

No comments:

Post a Comment