Sunday, 30 September 2018

Muddin PDP ta bani takarar shugaban kasa to Buhari cewa zai yi ya hakura dan bazai iya karawa dani ba>>Datti Baba Ahmed

Daya daga cikin masu neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Datti Baba Ahmed yayi kaca-kaca da Buhari inda yace yafi Buharin komai.


Da yake hira da wakilin jaridar Punch, Baba Ahmed ya bayyana cewa, idan PDP ta tsayar dashi takarar shugaban kasa to zai yi mamakin ace Buhari ya ci gaba da neman kujerar shugabancin kasarnan, yace muddin hakan ta faru to Buhari cewa zai yi ya fasa zarcewa dan ba zai iya karawa dashiba.

Yace shi ba irin Buhari bane, Buhari yana so ayi noma ne yayin da shi kuma yake so ayi ilimi, karfafawa mutane, masana'antu da kimiyya, Buhari akwai son nuna banbancin addini shi kuma na kowane, Buhari kama mutane yake yana daurewa, shi kuma zai warware matsalolin kasarnanne.

Dan haka yace Buharin ba zai iya karawa dashi ba.

No comments:

Post a Comment