Wednesday, 12 September 2018

MUHIMMIYAR SANARWA DA FADAKARWA DAGA MALAM AMINU DAURAWA>>TSAKANIN IYALI DA IYAYE

NA DAUKI KUSAN TSAWON SHEKARU TALATIN, INA SHIGA HARKAR AURE, DA SASANTA TSAKANIN MAAURATA, NAJI MATSALOLI IRI IRI, NAYI NASARAR SULHUNTA MAAURATA DA YAWA, WASU DA YAWA NA KASA SHAWO KAN MATSALAR.


DAGA CIKIN WANDA YAFI BANI WAHALA, SHINE IDAN AKA SAMI MATSALA DA RASHIN FAHIMTA TSAKANIN MATAR MUTUM DA MAHAIFIYARSA KO DA MAHAIFINSA, MUNA SHAN WAHALA SOSAI WAJAN WARWARE MATSALAR, WANI LOKACIN SAI  DAI MU HAKURA KAWAI MUYI MUSU ADDUA. 

WANNAN YASA NA DAUKE FAYIL DIN WANNAN MATSALA ZAN WALLAFA LITTAFI AKAI DOMIN MU TARU MU SHAWO KAN WANNAN MATSALA KO MU RAGE TA, HAR AN WAYI GARI WASU MATA DA YAWA BASU SON AURAN MAI IYAYE MUSAMMAN UWA, WASU MATA SUNA KIRAN TA VIRUS WASU SUNA KIRAN TA MATSALA, DA SUNAYE IRI IRI, DUK MAI YA JAWO HAKA.? 

MATSALAR IYAYAN MUTUM DA IYALINSA BA SABUWA BACE, DOMIN KA A ZAMANIN SAHABBAI AN SAMI IRIN WANNAN DA YAWA, KAMAR KISSAR ABDULLAH DAN UMAR, (RA,) DA MAHAIFINSA UMAR DA KUMA MATARSA WACCE S. UMAR YA UMARCESHI YA SAKETA, KUMA A KARSHE SAKIN YA FARU BAYAN ANNABI SAW YA SHIGA MAGANAR. 
WANNAN LITTAFI DA ZAM WALLAFA BAWAI KARATU ZALLA ZAN KAWO. BA KISSOSHI DA LABARAI DA SUKA FARU, NA  JITUWA KO RASHIN TA DA AKA SAMU TSAKANIN IYAYAN  MIJI DA MATARSA, NA KALLI WANNAN LAMARI TA BANGARE GOMA
NA DAYA.  MASALI, NA IYAYAN DA SUKA SAMI FAHIMTAR JUNA DA IYALI BABU MATSALA
NA BIYU INDA AKA SAMI MATSALA DA UBA, SHI BAYA SON AURAN, AMMA UWA TANA SO. 
NA UKU, INDA UBA YAKE SON AURAN AMMA UWA BATA SO.
NA HUDU INDA DUKA  SU BIYUN BASA SON AURAN,  AMMA SHI MIJIN YANA SON. MATARSA.

NA BIYAR,  INDA UWAR MIJIN TAKE SON MATAR AMMA SHI MIJIN BAYASO.
NA SHIDA INDA SHI UBAN YAKE SON AURAN AMMA SHI DAN BAYASO. 
NA BAKWAI,  IYAYAN DA SUKE TAKURAWA DANSU YA AURI MATAR DA BAYASO.
NA TAKWAS IYAYAN DA SUKE HANA DANSU YA AURI MATAR DA YAKE SO
NA TARA. AKAN SAMI SABANI TSAKANIN IYAYE, KOWA YA KAWO WA DANSA MATAR DA YAKE SO YA AURA.

NA GOMA SAMUN GOYAN BAYAN DAYA DAGA CIKIN MAHAIFA GA DAYA DAGA CIKIN 

IYALIN MAI MACE FIYE DA DAYA. WATO IYAYE SU GOYI BAYAN DAYA DAGA CIKIN. MATANSA SU TAYA TA KISHI.

YAYA MUTUM ZAIYI IDAN IYAYAN SA SUN. MATSA MASA YA SAKI MATARSA, ALHALIN SHI KUMA YANA SON TA.? 

YAYI MUTUM ZAIYI IDAN DAYA DAGA CIKIN MAHAIFANSA YA TILAS TASHI YA SAKI MATARSA, KUMA DA YAN YACE KADA YA SAKE TA? MAGANAR WA ZAI DAUKA DAGA CIKI? 

IDAN BABANKA YA ZABO MAKA MATA, BABARKA TA ZABO MAKA MATA WACCE ZAKA AURA DAGA CIKI.?

IDAN MUTUM YANA ZAMAN LAFIYA DA MATARSA GA YAYA A TSAKANIN SU KUMA MAHAIFIYARSA KO MAHAIFINSA YACE LALLAI SAI AN RABU YAYA ZA AYI.?

DUK WANDA YAKE DA LABARI IRIN DAYA DAGA CIKIN WANNAN YA TURO MANA TA WANNAN ADRESHI. www.aidaurawa@gmail.com 

DA FATAN ALLAH YA WARWARE MANA MATSALOLI DA SUKE DAMUNMU A ZAMANTAKEWA DA IYALI DA IYAYE.

No comments:

Post a Comment