Monday, 10 September 2018

Mulkin shafaffu da mai ya kusa zuwa karshe>>Saraki

Kakakin majalisar dattijai kuma me muradin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019 me zuwa, Bukola Saraki ya bayyana cewa mulkin mayar da wasu shafaffu da mai ya kusa zuwa karshe.


Saraki yayi wannan maganane a jihar Benue inda ya halarci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar sanata Barnabas Gemade me wakiltar Benue ta arewa maso gabas a majalisar tarayya.

Ya kara da cewa, yaje Benue dinne dan ya halarci bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Gemade sannan kuma ya gana da delegates din PDP na jihar akan maganar fitowarshi takara kamar yanda jaridar Guardian ta ruwaito.


No comments:

Post a Comment