Friday, 28 September 2018

Mura ta kashe mutane dubu 80 a Amurka

A lokacin sanyin da ya gabata mutane dubu 80 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mura a Amurka.


Shugaban Cibiyar Kula Tare da Hana Yaduwar Cututtuka ta Amurka (CDC) Dr. Robert Redfield ya ce, a lokacin sanyin da ya gabata cutar mura ta kashe mutane dubu 80.

Redfield ya kara da cewa, a shekaru 40 da suka gabata wannan ne lokacinda cutar ta mura ta janyo asarar rayuka mafi yawa inda ya yi kira da a yi allurar riga-kafin cutar ta mura.

A tsakanin shekarun 1918-1920 sama da mutane dubu 500,000 ne suka mutu a Amurka sakamakon wata cutar mura da ta zama annoba a kasar.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment