Thursday, 13 September 2018

Mutumin da ya hau tangaraho yace ba zai sauko ba sai Buhari ya sauka daga mulki, ya sauko kasa dan kashin kanshi

Mutuminnan da ya hau tangaraho a babba birnin tarayya, Abuja ya ce bazai sauko ba sai shugaba Buhari ya sauka daga kan mulki ya dai gaji dan radin kanshi ya sauko daga kan tangarahon bayan awanni 24 da hawanshi.


Mutumin me suna Nura Iliyasu ya yadda da saukowa kasa da sharadin cewa za'a barshi yayi magana da 'yan jaridu, da farko dai an yita fama dashi ya sauko ya kiya amma daga baya, a yau Alhamis da misalin karfe 11:25 sai gashi ya sakko da kanshi.

Iliyasu ya shaidawa manema labarai cewa, shifa gaskiya Buharine beso ya ci gaba da mulki saboda irin yanda ya kawo yunwa da talauci a kasarnan ya kamata ya sauka kada ya zarce.

Iliyasu ya kara da cewa, bashi da tabin hankali kamar yanda wasu ke fada, ras yake da hankalinshi.

No comments:

Post a Comment