Tuesday, 4 September 2018

Na yi mamakin tafiyar Ronaldo daga Madrid: Yanzu karfinsu ya ragu>>Messi

Tauraron dan kwallon kafar Barcelona, Lionel Messi ya bayyana cewa, bai taba tunanin abokin hamayyarshi, Ronaldo zai bar Real Madrid ba kuma yayi mamakin da ya koma Juventus.


Marca ta ruwaito, Messi na cewa, Real Madrid kungiyace me kyau kuma suna da 'yan wasa kwararru amma tafiyar Ronaldo dole tasa karfinsu ya ragu, ya kuma ce bai taba kawowa a zuciyarshi Ronaldon zai koma Juventus ba amma itama kungiyace me kyau suna da gogaggun 'yan wasa wanda a yanzu da suke da Ronaldo zasu iya daukar kofin zakarun turai.

Messi ya kuma yi magana akan cewa bashi da niyyar barin Barcelona, yace yazo kungiyar tun yana dan shekaru 13, dan haka ta zame mai kamar gida kuma ya haifi 'ya'yanshi anan kuma suna da abokai haka kuma anan suke makaranta dan haka bazai bar Barcelona ba.

Messi yayi bayanin cewa bazai kai shekaru 40 yana buga kwallo ba saidai be bayyana abinda zaiyi ba idan yayi ritaya daga taka leda inda yace besan me zaiyi ba amma idan lokacin yayi zamu gani.


No comments:

Post a Comment