Wednesday, 5 September 2018

Ni ba barawo bane idan kuma akwai me shedar na taba sata to ya fito ya bayyana>>Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugabancin kasarnan karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa shi fa ba barawo bane.


Ya bayyana hakane a jihar Ekiti inda ya gana da delegates da zasu yi zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP ya kuma bukaci su zabeshi saboda yana da aniya me kyau ta kawo ci gaba a kasarnan, kamar yanda Premiumtimes ta wallafa.

Atiku yace, yasha fadin cewa, shi ba barawo bane idan kuma akwai wanda yake da shedar cewa ya saci kudin gwamnati to ya fito ya bayyana, amma har yanzu shiru.


No comments:

Post a Comment