Sunday, 16 September 2018

Pogba yana son ci gaba da zama a United>>Mourinho

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce dan wasan tsakiya Paul Pogba "bai taba gaya mini cewa yana son barin kulob din ba."


Pogba bai nuna wata alama ta ci gaba da zama a Manchester tun bayan da Faransa ta dauki kofin duniya, sai dai Mourinho ya dage cewa dan asan "yana son ci gaba da zama" a nan.

"Zan yi tsokaci ne kawai kan abin da yake zahiri a gare ni, ba abin da na ji ko na karanta ba," in ji dan kasar ta Portugal.

Amma Pogba ya ce za a ci tarar sa idan ya tattauna game da hakikanin abin da yake ransa bayan ya zura kwallo a wasan da suka doke Leicester.

Dan wasan dan kasar Faransa ba ya dasawa da masu tafiyar da United tun kakar wasa ta 2017-18.

Sai dai ana ta rade-radin zai koma Barcelona tun bayan rawar ganin da ya taka a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha, ciki har da kwallon da ya zura wasan su da Croatia.

Da yake magana kafin wasan su a Jamus na gasar lig ta Faransa, Pogba ya ce: "A yanzu haka makomata tana Manchester. Ina buga wasa a can a yanzu, amma ban san abin da zai faru ba nan da watanni kadan masu zuwa."

Amma Mourinho ya yi watsi da tsokacin da Pogba ya yi, yana mai cewa "wannan matsalar dan wasan ce da kuma dangantakarsa da 'yan jarida".
BBChausa.

No comments:

Post a Comment