Sunday, 16 September 2018

Rasha ta fara daukar matakan karya darajar dala a fadin Duniya

Rasha ta bayyana cewar ya zama wajibi ga dukkanin kasashe da su dauki matakan rage amfani da dala a cinikayya tsakaninsu.


Mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dimitriy Peskov, ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu a Moscow babban birnin Rasha inda ya bayyana cewar Rasha, China da Turkiyya sun dauki matakan rage amfani da dala a yayin gudanar da kasuwanci a tsakkaninsu.

Ya kara da cewa domin rage karfin dala a duniya kasashe da dama a fadin duniya na tattaunawa da juna inda suke aminta akan gudanar da kasuwanci a tsakaninsu ta amfani da nau’in kudaden kasashensu maimakon dala.

Peskov ya jaddada cewa a yayinda kasashen Nahiyar Turai, gabashi da gabas ta tsakiya ke kokarin aiyanar da yarjejeniya a tsakaninsu domin rage hakincin da dala take dashi a duniya, Rasha ta dauki wannan matakin da muhinmanci.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment