Tuesday, 25 September 2018

Real Madrid: Isco na fama da cutar appendicitis

Kulub din Real Madrid ya sanar da cewa likitoci sun gano cewa dan wasan gaban kwallon kafa Isco na fama da matsananciyar cutar appendicitis, kuma ana bukatar yi masa tiyata don magance ta.


Dan kwallon, dan tawagar Spaniya ya ci kwallon farko a wasan da Real Madrid suka ci Roma kwallaye uku a wasan Gasar Zakarun Turai a makon da ya gabata.

Isco, mai shekara 26, ya buga wasanni shida a wannan kakar, amma ba zai samu damar buga sauran wasanni na gaba ba, ciki har da wanda kungiyarsa za ta fafata da Sevilla a gasar La Liga a Laraba.

A sanarwar da Real Madrid ta fitar, ba ta fadi tsawon lokacin da dan kwallon zai dauka kafin ya ji sauki ba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment