Monday, 17 September 2018

Rikici ya barke a jam'iyyar APC

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta fada rikici a reshen ta da ke jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin kasar.


Hakan na faruwa ne bayan wasu daga cikin masu so su tsaya takarar gwamna a zaben 2019 karkashin jam'iyyar sun yi zargin cewa shugabannin jam'iyyar na so su bai wa gwamnan jihar tikitin sake takara ba tare da zaben fitar da gwani ba.

Tsohon ministan lafiya, Dr Muhammad Pate da takwaransa na 'yan sanda, Alhaji Yabubu Lame sun shaida wa BBC cewa jam'iyyar na so ta yi musu yankan-baya.

"Mun samu labarin cewa [jagorancin jam'iyya a jiha] ya amince ya tsayar da gwamna ba hamayya. Idan aka yi zabe cikin adalci za mu yarda amma idan ba a yi adalci ba za mu tafi inda za a yi mana adalci," in ji Dr Yakubu Lame.

Shi ma Dr Pate ya ce, "Tun da jam'iyya ta ce 'yar tinke za a yi wajen tsayar da shugaban kasa, sannan a wasu jihohi kamar su Legas da Kano, su ma ake maganar za su bi sahu, ya kamata mu ma a Bauchi a yi haka. Ba gaskiya aka shirya ba idan aka ce wakilai [delegates] ne za su yi zabe."

Ya yi kira ga shugabancin jam'iyyar na kasa baki daya ya dauki matakin gyara wannan matsala.

Sai dai shugaban jam'iyyar APC na jihar Bauchi Alhaji Uba Nana ya ce sun dauki matakin yin zabe na wakilai ne domin a zauna lafiya.

A cewarsa."Tun a tuin taron kwamitin koli na jam'iyya aka yarda a yi 'yar tinke wajen fitar da shugaban kasa sannan aka amince jihohi su zabi hanyar da ta fi musu kyau. Don haka wanna ba matsala ba ne."

Baya ga Bauchi, jihohi da ama na fama da irin wannan matsala, lamarin da masu sharhi kan siyasa ke ganin zai iya shafar nasarar jam'iyyar a zabukan da ke tafe.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment