Sunday, 2 September 2018

Rikici ya kunno kai a PDP a Kano

Bayan sauke shugabannnin jam'yyar PDP da uwar jam'iyyar ta kasa ta yi, wasu jiga-jigan jam'iyyar a Kano sun nuna rashin gamsuwarsu da wannan matakin.


Da alama tsugune ba ta kare ba a siyasar Kano, domin wannan matakin ya janyo rarrabuwar kawuna tsakanin jagororin jam'iyyar PDP a Kano.

A bangare daya, Mallam Ibrahim Shekarau da Aminu Wali da Bello Hayatu sun ce ba za su amince da matakin uwar jam'iyyar ba.

Mallam Ibrahim Shekarau ya bayyana matsayarsu a wata hira da yayi da maneman labarai.

"Ni Ibrahim Shekarau, a madadi na da sauran jagorori da shugabanni na jam'iyyar PDP ta jihar Kano, na godiya ga magoya bayan jam'iyyar saboda hakuri da biyayya da ake nunawa ga jagorancin jam'iyya."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment