Friday, 28 September 2018

Ronaldo ya taya Modric da Salah murna: saidai yace kwallonshi ce tafi kyau

Tauraron dan kwallon Juventus, Cristiano Ronaldo yayi magana a karin farko akan kyautukan gwarazan kwallon FIFA da aka bayar a ranar Litinin din da ta gabata a birnin Landan na kasar Ingila inda be samu zuwa ba.


Luka Modric ne ya lashe kyautar gwarzon FIFA na kakar 2017/18 sai kuma Mohamed Salah ya lashe kyautar cin kwallon da ta fi kyau a kakar wasan.

Ronaldo ya taya Tsohon abokin aikinshi, Modric murna ta dandalinshi na sada zumunta inda yace, ina taya Luka Modric murnar samun wannan kyauta.

Ya cewa Salah, Salah ya cancanci lashe kyautar Puskas, kwallon da yaci me kyauce.

Saidai da wasu daga cikin masoyan na Ronaldo suka tambayeshi wai wace kwallo tafi kyau tsakanin wadda yaci da ta sauran? 

Sai ya ce, maganar gaskiya, kada ku yaudari kanku, kwallon da naci itace tafi kyau.

Ya kara da cewa, Kyautuka ne aka bayar kuma inadasu da yawa, ina wasa dan samun nasara ne bawai dan cin kyautuka ba, na kasance wanda yafi kowa na tsawon shekaru 15 kuma ina alfahari da nasarorin dana samu.


No comments:

Post a Comment