Thursday, 13 September 2018

Ronaldo zai bude Otal a birnin Paris

Tauraron dan kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo zai bude Otel me suna CR7 a birnin Paris na kasar Faransa, wannan otal din dai zai zama na shida kenan a cikin jerin otal din da yake dasu a kasashen Duniya.


Za'a bude otal dinne a shekarr 2021 idan Allah ya kaimu a day daga cikin biranen da aka fi ziyarta a Duniya watau Paris kamar yanda Ronaldon ya bayyanawa manema labarai.

A yanzu haka dai Ronaldo nada otal guda 2 ne dake biranen Lisbon da Funchal da ya bude a shekarar 2016 wanda ya bude da hadin gwiwar wani rukunin wani kamfanin kasar Portugal me suna Pestana, inda Ronaldon yake da kaso 50 cikin 100 na jarin otaldin.

A shekarar 2020 Ronaldo zai bude wasu karin otaldin guda uku a biranen Madrid da New York da Marrakech, kamar yanda kafofin labarai da dama suka ruwaito.

No comments:

Post a Comment