Tuesday, 25 September 2018

'Ronaldo zai koma Real Madrid'

Bayan da aka kammala bayar da kyautukan gwarazan 'yan kwallon hukumar kwallon kafa ta Duniya, FIFA a birnin Landan na kasar Ingila, shugaban kungiyar Real Madrid, Florentino Ferez ya bayyana cewa, Cristiano Ronaldo zai koma Madrid din.


Perez ya yabi Ronaldo a wata hira da yayi da manema labarai inda yace Ronaldo dan wasane wanda a koda yaushe zai kasance a zukatan masoya kungiyar Real Madrid kuma yayi amannar cewa wata rana Ronaldon zai koma kungiyar ta Madrid.

Saidai ya tabbatar da cewa, Luka Modric ne dama can ya cancanta ya lashe kyautar gwazon dan kwallon FIFA saboda ya jagoranci Madrid zuwa cin kofin zakarun turai sau 3 a jere sannan kuma ya jagoranci kasarshi zuwa wasan karshe na cin kofin Duniya 2018.

Ya karkare maganarshi da cewa Madrid ce ke da 'yan wasa da suka fi kowane 'yan wasa kyau a tsakanin kungiyoyin kwallo na Duniya.

No comments:

Post a Comment