Saturday, 29 September 2018

RUNDUNAR 'YAN SANDAN NIJERIYA TA YAYE SABBIN JAMI'AN TSARO

Bisa Umarnin shugaban Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari na diban sabbin 'yan sanda dubu goma (10,000) yau juma'a 28-9-2018 rundinar 'yan sanda karkashin jagorancin babban sufetan 'yan sanda na Kasa IGP Ibrahim K. Idris ta yaye sabbin jami'an 'yan sanda kashi na farko bangaren Specialist wadanda suka kammala karban horo a kwalejin horar da aikin 'yan sanda na Nigeria


Shugaban 'Yan sandan Nigeria IGP Ibrahim K Idris ta bakin wakilanshi, a yayin taron yaye 'yan sandan yayi godiya ga shugaban Nigeria Muhammadu Buhari bisa umarnin da ya bayar na diban sabbin 'yan sanda, ya kuma gargadi sabbin jami'an 'yan sandan da suka kammala karban horo masu mukamin constable da su zama jami'ai masu gaskiya da rikon amana da gudanar aiki bisa dokar aikin 'yan sanda.
Rariya.

No comments:

Post a Comment