Monday, 17 September 2018

Sanata Akpabio yaki yin amfani da Lema yayin da ake ruwan sama saboda alamace ta PDP

Sanata Godswill Akpabio wanda kwanannan ya canja sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC me mulki yaki yin amfani da Lema a yayin da yake halartar wani taron nuna goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari a jiharshi ta Akwa Ibom duk da cewa ana sheka ruwan sama.


Ya rika daga tsintsiya sama yayin da ruwa ke jikashi, rahotanni sun bayyana cewa yaki yin amfani da lemarne saboda alamace ta jam'iyyar adawa ta PDP.

Saidai wasu sun sokeshi akan wannan abu inda sukace be kamata a siyasantar da komai ba.


No comments:

Post a Comment