Friday, 28 September 2018

SHARWARWARI>>Daga Malam Aminu Daurawa

🌹= Kafin kayi rubutu kayi nazari akai;
 🌹= Kafin kayi magana kayi tunani akai; 🙉
 🌹= Kafin ka yanke hukunci kayi bincike akai;
 🌹= Ba kowacce magana ake yarda da ita ba; 
 🌹= Kuma ba kowacce ake karyatawa ba;
 🌹= Kafadi Alkairi ko kayi shiru;


 🌹= Ka yawaita aikata Alkairi fiye da sharrii;
 🌹= Ka yawaita kyakyawar addu'a fiye da mummuna;
 🌹= Ba kowa bane mutumin kirki kuma Ba kowa bane mutumin banza;
 🌹= Kada ka zagi kowa kuma in an zageka kayi hakuri yafi;
 🌹= Kafun ka roki wani abu gun Allah ka yimasa godiya akan abunda kake dashi;
 🌹= Ka yawaita neman gafara agun Allah kuma kar kacuci kowa;
 🌹= Ka yawaita yiwa Annabi muh'd (s.a.w) salati a kullum kuma akoda yaushe saboda bakada kamarshi;
 🌹= Kada kaji haushi idan kayi post a whatsapp, face book , instagram, mai ma'ana idan ba'ayi maka comment ba don ba kowa ne keson irin post dinka ba;
 🌹= Kada ka fifita kayan shaidan fiye da na Allah ;
 🌹= Kada kayi yaudara a soyayya saboda alhaki kyaiwkuyo ne Kaima watarana za'ayi maka ko ayiwa wani naka;
 🌹= Idan kaga wani mai mummunar tarbiya Kada kayi saurin la'antarsa kai dai kayi masa addu'a ko kayi shiru; 
 🌹= Idan kaga mabukaci ka taimakeshi Allah zai biyaka;
 🌹= Ka yawaita sadaka saboda tana yaye zunubai;
 🌹= Ka taimaki tsoho ko tsohuwa , koda ba naka bane kaima watarana za'a taimaki naka;
 🌹= Ka sada zamunci domin yana kara nisan kwana kuma yana kara Arziki;
 🌹= Allah yakawo mana dauki ya kuma sa mudace;

No comments:

Post a Comment