Tuesday, 11 September 2018

Shehu Sani ya bayar da labarin yanda wasu matasa masu fama da kansu suka ce ya basu damar yin karyar cewa sune suka sai mishi fom

A lokacin da ake tsaka da yayin sayawa 'yan siyasa ciki hadda masu rike da mukamai fom din tsayawa takara, Sanata Shehu Sani ya fito yace shi be yarda da irin wannan yaudarar ba.Sanata Shehu Sani ya bayar da labarin yanda wata kungiyar matasa da yace suna fama da kansu suka sameshi sukace ya basu dama su yi karyar cewa sune suka saya mishi fom din sake tsayawa takara amma sai yace musu ya gode domin baya son shiga cikin yayin siyasayar yaudarar da ta kunno kai.

Yace sun amince suka barshi.

Sanata Shehu Sani ya kuma bayar da labarin yanda wani abokinshi dan siyasa ya bashi hankici da yaji wai ya shafa a fuskarshi lokacin da yake mayar da fom dinshi na tsayawa takara dan yayi hawayen karya, yace anan ma be yardaba yace mishi shi dan gwagwarmayane ba me wasan kwaikwayo ba.

No comments:

Post a Comment