Monday, 10 September 2018

Shekarau Ya Karbi Katinsa Na Zama Memban APC

A safiyar yau ne tsohon gwamnan jihar Kano Dakta Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano, Wazirin raya kasar Nupe, Ya karbi katin shedar zama dan jamiyyar APC a mazabar sa dake Unguwar Giginyu tare da rakiyar dubban magoya bayan sa.Wannan na zuwa kwana daya tal da yanke hukuncin sauya sheka daga jamiyyar PDP mai adawa zuwa jamiyyar APC mai mulki, Masha Allah Sardaunan muna kara maka barka da zuwa da fatan alkairi.

Allah ya kara hada mana kan shugabannin mu yasa wannan gamayyar za ta kawowa al'ummar jihar Kano alkairi da zaman lafiya har da kasa baki daya.
Rariya.

No comments:

Post a Comment